Labarai
Masarautar Kano ta Gidan Nassarawa ta Sarki Alh. Aminu Ado Bayero ta sanar da dakatar da shirinta na gudanar da hawa a lokacin bukukuwan Babbar Sallah na shekarar 2025, bayan nazari da shawarwari tare da hukumomin tsaro a cewarta.

Wannan na cikin sanarwar da Sakataren Masarautar, Malam Awaisu Abbas Sanusi ya fitar, inda ya ce daukar wannan mataki ya zama dole saboda rahotannin tsaro da ke nuna yiwuwar tayar da zaune tsaye daga wasu batagari.
Masarautar ta ce wannan dakatarwar ta yi daidai da dokar hana hawan dawakai da aka shimfiɗa tun ƙaramar Sallah, inda aka hana kowanne irin hawan da zai iya zama barazana ga zaman lafiya.
A ƙarshe, masarautar ta roƙi alʼumma su dage da addu’ar neman zaman lafiya ga Kano da kasa baki daya.
Wannan dai na zuwa ne bayan yan sanda sun sanar da haramtawar a wanni kadan bayan masarautar Kofar Kudu ta umarci a soma shiri.




