An hangi Alkali Abubakar Salihu Zaria a cikin rumfar mai shayi ɗauke da babban saqo.

Alkali Abubakar Salihu Zaria sanannen malamin addinin Muslunci ne, kuma mai da’awa cikin hikima da raha.
Yana mai cewa yau kuma za’a yi mamakin ganinmu a rumfar mai shayi wato malam Muhammad Sani dauke da muhimmin saqo.
A cewar sa, mun sami wani mummunan labari ne game da mai sayar da shayi a wannan waje wato Muhammad Sani mai shayi, don haka muka zo mu yi masa nasiha wanda kuma ya shaida mana cewa ya ɗauki wannan nasiha hannu bibbiyu.
Ya qara da cewa shi dai Muhammad Sani yana yin kasuwanci da wata qa’ida marar kyau wadda Allah S.W.A bai yarda da ita ba, kuma Annabi Muhammad S.A.W bai yarda da ita ba.
Yana mai cewa ita wannan qa’ida dai ita ce; Mun sami labarin Muhammad Sani yana sayar da shayi tare da bread, sharaɗin sayen shayi a wajen shi shine sai ka haɗa da bread sannan zai sayar maka da shayin shi.
Malam ya qara da cewa mutane suna kokawa akan hakan sosai da sosai, don haka sai muka ga babu inda ba’a yin nasiha, lallai ya zame mana wajibi mu zo wannan wajen domin muyi masa nasiha tare da dukkan mai halaye irin wannan.
Malam ya ci gaba da cewa almuhimmi anan shine ya kamata ƴan kasuwa su lura cewa akwai mutane masu larura, akwai mutanen da iya ruwan shayin suke bukata za su sha magani da shi ko wata bukata makamancin hakan.
Ya qara da cewa Sannan akwai matafiya, akwai masu azumi wanda iya ruwan shayin suke bukata don ya warware musu hanji kamar yadda likitocin duniya suke yi ittifaqi kuma suke bada shawara akan muhimmancin yin hakan.
Wasu kuma iya kudin ruwan shayin suke da shi, idan ka ce sai sun hada da bread to sai dai su zauna ba tare da sun sanya komai a cikin cikin su ba, wanda hakan zai iya bayuwa ga haihuwar wata cutar a jikin su, a cewar malam.
Malam Abubakar Salihu Zaria ya ce, dole sai mun tausaya ma junanmu Sannan Allah zai tausaya mana, idan muka zama masu jin kai, masu gaskiya da adalci hakika Allah zai zama gata kuma zai sanya albarka a cikin kasuwancinmu da sauran lamurran rayuwar mu.
Malam ya ce wannan nasiha ce, duk wanda muka ɓata masa rai yayi mana aikin gafara, ba mu yi wannan nasihar/aikin don cutarwa ko ɓatanci ko cin mutuncin wani mutum ba.
Hakanan a bangaren Muhammad Sani mai shayi ya amsa cewa ita dai wannan qa’idar tasa tuni ya karya ta, kuma yayi watsi da ita, duba da irin nasihar da shehin malamin yayi masa.
Ya ce yana godiya game da irin hanyar da malamin ya bi domin yi masa nasiha cikin hikima, sannan ya yi kira ga ƴan kasuwa cewa wannan babbar nasiha ce wadda ya kamata kowa ya karɓa hannu bibbiyu.
Madallah da malam tare da godiya akan ayyukan alkhairi irin na malam cewar wani mutum a cikin rumfar shayin.




