Birtaniya ta yi barazanar kara daukar mataki kan Isra’ila idan shawarar tsagaita bude wuta a Gaza ta gaza

Sakataren Harkokin Wajen Biritaniya, David Lammy, ya yi Allah wadai da rikicin jin kai a Gaza, yana mai cewa Biritaniya na iya daukar karin mataki kan Isra’ila idan ba a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta don kawo karshen yakin a yankin Falasdinawa ba.
Da yake magana a gaban kwamitin harkokin Wajen Majalisar a ranar Talata, Lammy ya kuma soki sabon tsarin rarraba tallafi a Gaza ta wata kungiya da Amurka da Isra’ila suka goyi baya, mai suna Gaza Humanitarian Foundation (GHF).
Daruruwan Falasdinawa sun mutu sakamakon harbin Isra’ila yayin da suke neman taimakon GHF a makonnin da suka gabata.
A ranar Talata, Lammy yayi Allah wadai da tashe-tashen hankulan mazauna yankin da kuma fadada matsugunan haramtacciyar kasar Isra’ila a yammacin gabar kogin Jordan, yana mai cewa “sun karya dokar kasa da kasa”.
Da aka matsa kan ko matsin lamba na Birtaniya akan Isra’ila ya sa gwamnatin Isra’ila ta canza halayenta, Lammy ya amince cewa canjin bai isa ba.
Duk da haka, ya kare tarihin London, ciki har da matakan baya-bayan nan da aka dauka akan Isra’ila da goyon baya ga hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya don ‘yan gudun hijirar falasdinu.




