Labarai
Shugaban kasar Nigeriya ya bada kyakkyawar shawara ga sauran shuwagabannin duniya musamman na Afrika.
Shugaba kasa Bola Tinubu ya bukaci a sake duba tsarin tafiyar da lamuran duniya musamman tsarin kudi da lafiya, yana mai jaddada bukatar adalci da hadin kai ga kasashe masu karamin karfi da masu tasowa, musamman a nahiyar Afirka.
Ya bayyana haka ne a taron kawancen BRICS karo na 17 dake gudana a birnin Rio de Janeiro, na Brazil.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa lalacewar muhalli, matsalolin sauyin yanayi, da rashin daidaito a fannin lafiya na daga cikin abubuwan da ke hana ci gaba da bunkasa duniya.
Shugaba Tinubu, wanda shugaban Brazil Luiz Inacio Lula Da Silva ya gayyata zuwa taron, ya ce Najeriya na goyon bayan matsayar BRICS kan bukatar a mayar da hankali kan ci gaban duniya a tsarin adalci.



