Labarai
Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da na’urarar rarraba hasken Wutar lantarki guda 500 a daukacin kanan hukumomi 44 dake fadin jihar.

Gwamnan ya ce wannan kaso na farko ne a yayinda nan gaba kadan za’a kaddamar da kaso na biyu a wani mataki na cika alkawuran da gwamnatin ta yi tun lokacin neman zabe.
Abba kabir yusuf ya umarci shugabannin kananan hukumomi da su samar da wani kwamiti da zai sanya idanu daga barazanar bata gari.




