Isra’ila ta yi luguden wuta a tashoshin jiragen ruwa, da tashar wutar lantarki a Yemen yayin da Houthawa suka harba karin makamai masu linzami

Sojojin Isra’ila sun yi luguden wuta a kan tashoshin jiragen ruwa guda uku da kuma wata tashar wutar lantarki a yankunan da ‘yan tawayen Houthi ke iko da su a Yemen, lamarin da ya sa kungiyar ‘yan tawayen ta harba karin makamai masu linzami zuwa yankin Isra’ila.
Sojojin Isra’ila sun ce a ranar Lahadi sun kai hari kan tashoshin jiragen ruwa na Hodeidah, Ras-Isa da as-Salif a gabar tekun Bahar Maliya da kuma tashar wutar lantarki ta Ras Kathib.
Harin da Isra’ila ta kai a daren Lahadi shi ne na farko a kan Yemen cikin kusan wata guda kuma ya biyo bayan ikirarin da sojojin suka yi na cewa sun tare wani makami mai linzami da Houthawa suka harba a farkon safiyar ranar.
Kungiyar ‘yan tawaye, wadda ke iko da yankunan da suka fi yawan jama’a a Yemen, ta mayar da martani ga hare-haren Isra’ila na baya-bayan nan ta hanyar harba karin makamai masu linzami zuwa Isra’ila a farkon safiyar Litinin.
Sojojin Isra’ila sun ce an harba makamai biyu daga Yemen, kuma sun yi ƙoƙarin tare makaman. Harin ya kunna siren a biranen Urushalima, Hebron.




