Labarai

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da cewa za ta fara ba da sufuri kyauta ga ma’aikatan gwamnati, masu ritaya da ɗalibai daga ranar Litinin, 7 ga Yuli, 2025, a ƙarƙashin shirin KSTS.

Darakta Janar na Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Kaduna (KADSTRA), Inuwa Ibrahim, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya ce za a ba waɗannan rukuni uku damar amfani da motocin kyauta har na tsawon watanni shida.

Ibrahim ya ƙara da cewa dukkan ɗalibai, ko na makarantar gwamnati ko masu zaman kansu, daga matakin firamare zuwa manyan makarantu, za su amfana da wannan tsari.

Ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin kokarin Gwamna Uba Sani na saukaka rayuwa ga ma’aikata, dalibai da tsofaffin da suka yi ritaya daga aiki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button