Hukumar Hisba ta rushe wani aure da take zargin an daurashi ba bisa ka’idaba

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta raba auren wasu matasa biyu da suka ɗaura wa kansu aure ba tare da sahalewar iyayensu ba, lamarin da ya janyo martani daga iyaye da masu ruwa da tsaki a harkar tarbiyya.
Rahotanni sun nuna cewa matashin da ake magana a kansa, Aliyu Mukhtar, ya ɗaura aure da budurwarsa Fatima, mazauniyar unguwar Yakasai a cikin birnin Kano, duk da cewa mahaifin matashin yaƙi amince masa da yin aure a wannan lokaci.
A cewar Aliyu, sun ɗauki wannan mataki ne bayan da iyayensu suka ƙi amincewa da bukatarsu ta aure, inda suka shirya kuma suka gudanar da ɗaurin auren a ɓoye ba tare da samun izini daga dangi ko waliyyan aure ba.
Sai dai wannan mataki da matasan suka ɗauka ya janyo martani daga iyayensu, wadanda suka garzaya hukumar Hisbah da ƙorafi, inda suka nemi hukumar ta binciki yadda aka yi har yara suka ɗaura aure ba tare da izini ba.
Bayan gudanar da bincike mai zurfi da kuma tantance bayanan da suka tattara, hukumar ta Hisbah ta tabbatar da cewa auren ba ya kan turbar da doka da tsarin addini suka tanada, wanda hakan ya sa ta yanke shawarar raba auren cikin gaggawa.




