Labarai

Ƴan majalisar wakilai bakwai daga jihar Akwa Ibom sun fice daga jam’iyyunsu na PDP da YPP zuwa jam’iyyar APC.

Yan majalisar da suka fice sun haɗa da Unyime Idem da Martins Esin da Paul Ekpo da Uduak Odudoh da Okpolu Etteha da Bassey Okon da kuma Emmanuel Ukpong-Udo.

Komawar yan majalisar zuwa APC ba ya rasa nasaba da ficewar gwamnan jihar daga jam’iyyar PDP a watan da ya gabata.

Tun da farko Gwamnan jihar ya fice tare da duka kwamishinoninsa da mutanen da ya naɗa muƙamai a gwamnatinsa zuwa jam’iyyar APC.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button