Mutukar Nigeria bata fito da sababbin tsare tsaren samun Karin kudin shigaba to tana cikin barazanar fadawa bakin talauci
IMF

Asusun bayar da lamuni na duniya (IMF) ya yi gargadin cewa kasafin kudin Najeriya na 2025 na fuskantar barazana mai tsanani, saboda raguwar farashin danyen mai, karancin samarwa, da matsalar aiwatar da manyan ayyuka.
A cikin sabon rahoton da aka fitar a ranar Laraba 02 ga Yuli ,2025. IMF ta yi hasashen cewa gibin kasafin kudi zai iya kai kashi 4.7 cikin 100 na GDP – fiye da abin da aka tsara.
Hukumar ta shawarci gwamnatin Najeria ta gaggauta sake duba kasafin kudinta, rage wasu kudade, da kara zuba jari domin kauce wa tabarbarewar tattalin arziki.
Rahoton ya bayyana damuwa kan karuwar bashin Najeriya, wanda ya haura kashi 53 cikin 100 na GDP, da kuma dogaron gwamnati ga kudaden mai.
IMF ta bukaci Najeriya ta kara fadada haraji da inganta hanyoyin samun kudin shiga, tare da bunkasa tallafi ga marasa galihu saboda kaucewa karuwar talauci da rashin abinci.
Sai dai, gwamnatin Najeriya ta bayyana kwarin guiwar cewa karin samar da danyen mai da gyare-gyaren cikin shekara za su taimaka wajen magance gibin kasafin kudi.
Rahoton ya kuma yabawa kokarin Najeriya wajen tsaurara manufofin kudade, da saukar da hauhawar farashi zuwa kashi 23.7 cikin 100 a watan Afrilu 2025



