Court ta aike da wasu matasa zuwa gidan yarin, bisa tuhumar aikata manyan laifuka da ake yi musu

Kotun Majistret mai lamba 22 karkashin jagorancin mai shari’a Ibrahim Sarki Ibrahim, ta aike da wasu matasa 2 gidan gyaran hali bisa zargin su da laifin hada baki da kutse fashi da makamin wayar salula, da kuma kisan kai
Kunshin zargin ya bayyana cewar matasan ana zargin su ne da hannu dumu-dumu a yawacin laifukan kisan kai da fashin waya da ake aiwatarwa a yankin sabuwar Sheka.
Masu bincike a cikin kunshin takaddun zargin sun bayyana wa kotun cewar, a watan da ya gabata waɗannan matasa sun hada baki sun je gidan wani mutum wanda ma’aikaci ne a jami’ar North west d ke nan Kano.
An yi zargin matasan sun haura gidan da talatainin dare suka yiwa mutumin fashi da makamin wayoyin salula guda biyu daga karshe gudun ko ya gane su hakan ya janyo suka caka masa wuka a ciki da wuya kuma nan take ya rasa ransa.
Wakilinmu buhari ali abdullahi ya ruwaito cewar matasan da ake zargi sun hadar da Amir Zakariyya da kuma Aliyu Hassan, sai kuma wasu matasa biyu da suka tsere dukkan su mazauna unguwar Sheka.
ko a makon da ya gabata dai babbar jojin jihar Kano ta ayyana cewar, duk wanda ya yi ƙwacen Waya indai ya yi amfani da makami duk kankantar sa to fa an aikata laifin fashi da makami.




