Mutane da dama sun bace bayan wani jirgin ruwa dauke da mutane 65 ya nutse a tsuburin Bali na kasar Indonesia

Akalla mutane hudu ne suka mutu yayin da wasu da dama suka bace bayan wani jirgin ruwa dauke da mutane 65 ya nutse a tsibirin Bali na kasar Indonesia, kamar yadda hukumomi suka bayyana.
Masu aikin ceto na neman mutane 38 bayan da jirgin KMP Tunu Pratama Jaya ya nutse jim kadan bayan barin tashar Banyuwangi ta Gabashin Java, hukumar bincike da ceto ta Indonesiya, Badan Nasional Pencarian Dan Pertolongan, ya fada a ranar Alhamis.
An ceto mutane ashirin da uku da suka tsira a matsayin wani bangare na ayyukan ceto, wanda ya haɗa da jiragen ruwa guda tara, a cewar jami’ai.
Shugaban ‘yan sandan Banyuwangi, Rama Samtama Putra, ya ce da yawa daga cikin wadanda suka tsira Saida suka suma bayan sun shafe sa’o’i suna yawo a cikin teku.
Shugaban kasar Indonesia Prabowo Subianto, wanda ke ziyara a Saudiyya, ya ba da umarnin gaggawa na daukar matakin gaggawa, Sakataren Majalisar Zartarwa Teddy Indra Wijaya ya bayyana a cikin wata sanarwa, yana mai cewa sanadin hatsarin ya kasance “mummunan yanayi.”
A shekarar 2018, fiye da mutane 150 sun nutse lokacin da jirgin ruwa ya kife a daya daga cikin mafi zurfin tabkuna a duniya a tsibirin Sumatra.




