Labarai
Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da kisan riƙaƙƙen ɗan bindigar da ya addabi wasu yankunan jihar.

Mai bai wa gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Ahmad Manga ya bayyana kisan Danbokolo a matsayin gagarumin nasara a yaƙi da matsalar tsaro.
Kacalla Danbokolo ya rasa ransa a wata arangama a ƙauyen Kurya, tsakanin jami’an sa kai na gwamnatin jihar Zamfara da mayaƙan ɗanbindigar.
Ana kallon mutuwar Danbokolo – wanda ake ganin a matsayin ubangidan Bello Turji – a matsayin cigaba a ɓangaren yaƙi da ƴanbindiga.
Donbokolo ya shafe shekaru masu yawa yana kai hare-hare yankunan jihar Zamfara tare da sace mutane domin neman kuɗin fansa.




