Ketare

Isra’ila ta yi luguden wuta a birnin Gaza bayan umartar Falasdinawa dasu fice daga yankin

Isra’ila ta kaddamar da hare-haren sama akalla 50 a fadin Gaza tare da mai da hankali musamman kan gabashin birnin Gaza bayan da sojojin suka bayar da umarnin tilasta ficewa, wanda ya haifar da fargabar karin farmaki.

Rundunar sojin Isra’ila ta kashe akalla Falasdinawa 68 a Gaza a ranar Lahadi, ciki har da akalla 47 a birnin Gaza da arewacin yankin, majiyoyin kiwon lafiya sun shaida wa Al Jazeera.

Ministan harkokin wajen Masar ya ce kasarsa tana aiki kan wata sabuwar yarjejeniya ta Gaza da ta hada da tsagaita wuta na tsawon kwanaki 60 a madadin sakin wasu fursunonin Isra’ila.

Yakin Isra’ila a kan Gaza ya kashe akalla mutane 56,500 kuma ya jikkata 133,419, a cewar Ma’aikatar Lafiya ta Gaza. An kiyasta cewa mutane 1,139 ne aka kashe a Isra’ila yayin hare-haren ranar 7 ga Oktoba, kuma fiye da 200 aka kama su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button