Akalla yara 66 sun mutu saboda rashin abinci mai gina jiki a Gaza yayin yakin Isra’ila

Aƙalla yara 66 sun mutu saboda rashin abinci mai gina jiki a Gaza a lokacin yaƙin Isra’ila, in ji hukumomi a yankin Falasɗinawa, suna la’antar tsauraran takunkumin Isra’ila da ya hana shigar madara, kayan abinci masu gina jiki da sauran tallafin abinci.
Sanarwar daga Ofishin Watsa Labarai na Gwamnatin Gaza a ranar Asabar ta zo ne yayin da dakarun Isra’ila suka tsananta hare-harensu a yankin, inda suka kashe akalla Falasdinawa 60, ciki har da mutane 20 a unguwar Tuffah ta birnin Gaza.
Sanarwar ta zo ne kwanaki bayan hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da yara (UNICEF) ta yi gargadin cewa yawan yaran da ke fama da rashin abinci mai gina jiki a Zirin Gaza na karuwa sannan Ta ce a kalla yara 5,119, masu tsakanin watanni 6 zuwa shekaru 5, aka shigar da su don jiyya saboda matsanancin rashin abinci mai gina jiki a watan Mayu kadai.
UNICEF ta ce adadin ya nuna kusan karin kashi 50 cikin 100 daga yara 3,444 da aka shigar a watan Afrilu, da kuma karin kashi 150 cikin 100 daga watan Fabrairu lokacin da aka samu tsagaita wuta kuma taimako yana shiga Gaza a cikin adadi mai yawa.




