Taiwo Oyedele ya ce gidaje a Najeriya da ke karbar Naira 250,000 ko kasa da haka a kowane wata ya kamata a cire su daga harajin kashin kansu.

Shugaban kwamitin shugaban kasa kan manufofin kasafin kudi da sake fasalin haraji, Taiwo Oyedel, ya ce a karkashin sabbin dokokin haraji, gidaje a Najeriya da ke karbar Naira 250,000 ko kasa da haka a kowane wata ya kamata a cire su daga harajin kashin kansu
Ya yi magana ne a cikin shirin ‘Siyasa A Yau,’ na gidan Talabijin na Channels, a ranar Alhamis, ‘yan sa’o’i kadan bayan Shugaba Bola Tinubu ya amince da wasu sabbin dokokin haraji guda hudu.
A cewarsa, makasudin sabbin dokokin da za su fara aiki daga watan Janairun shekarar 2026, ba wai don kara haraji ba ne, illa dai tada hankulan al’ummar kasar da kuma bin diddigin masu kaucewa biyan haraji.
Oyedele ya bayyana cewa sabbin dokokin za su kuma ba da kariya ga ‘yan kasuwa da tabbatar da cewa gwamnati ba za ta sanya harajin talauci ba, ya kara da cewa sabbin dokokin sun dogara ne akan inganci, mai da hankali kan ci gaban alumma.




