Labarai

Kwamishinan Ruwa na jihar Kano yayi murabus

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da murabus ɗin Kwamishinan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa na jihar, Umar Haruna Doguwa.

 

 

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu

 

 

Hon. Doguwa ya miƙa takardar murabus ɗinsa a hukumance ranar Litinin, 2 ga Maris, 2026, wanda ya fara aiki nan take.

 

Gwamna Yusuf ya bayyana godiyarsa bisa jajircewa, biyayya da sadaukarwar da Doguwa ya nuna wajen hidimtawa al’umma da gwamnatin jihar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button