Ketare

Kafofin yaɗa labarai a Iran sun ce gwamnati ta fara buɗe filayen jiragen sama a gabashin ƙasar yayin da sannu a hankali al’amura ke komawa daidai.

An dawo da layukan intanet sannan shaguna ma suna buɗewa.

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren Isra’ila a hukumance ya zarce ɗari shida.

Sun haɗa da shugaban dakarun juyin juya hali na Iran da za a yi jana’izarsa a yau.

Jibi Asabar kuma za a yi jana’izar sauran kwamandoji da ƙwararrun masana kimiyya da suka mutu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button