Labarai
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya nada Malam Adamu Yusuf Tofa a matsayin Babban Mai taimaka masa na musamman kan Ilimin Tsangaya, da kuma Surajo Ahmad Chedi a matsayin mai bashi shawara kan ci gaban alʼummar karkara.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da Babban Darkatn Yaɗa Labaran Gwamnam Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.
Sanarwar ta ce Malam Tofa tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Tofa ne, sannan kuma kwararre a ilimin addinin Musulunci da tsarin Tsangaya.
Sanarwar ta Kara da cewa gwamnan ya yi waɗannan nade-naden domin kara shigowa da mutane a tafiyar gwamnati, musamman jama’ar karkara da masu bukata ta musamman.


