Kisan Mata da ‘Ya’yanta: Kogunan Ƙasar Hausa Ya Yi Allah-Wadai, dafaruwar lamari tare da mika ta’aziyya ga iyalan mamatan

Mai Unguwar Gandun Sarki kuma Kogunan Ƙasar Hausa, Alhaji Da’u Abubakar, ya bayyana matuƙar alhininsa da kaɗuwarsa kan mummunan kisan gillar da aka yi wa wata uwa da ‘ya’yanta shida a jihar Kano.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Alhaji Da’u Abubakar ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, inda ya bayyana kisan a matsayin wani aiki na dabbanci kuma abin takaici wanda ya girgiza al’umma.
“Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya jikan mamatan da rahama, Ya sa aljanna ce makomarsu, kuma Ya bai wa iyalai da ‘yan uwa haƙurin jure wannan babban rashi,” in ji sanarwar.
Kogunan Ƙasar Hausa ya kuma yaba wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa nuna damuwa da kulawa da ya yi kan lamarin.
Haka kuma, ya jinjinawa rundunar ‘yan sanda bisa ƙwazon da suka nuna wajen gudanar da bincike cikin gaggawa, wanda ya kai ga kama waɗanda ake zargi da hannu a wannan aika-aikar.
A ƙarshe, Alhaji Da’u Abubakar ya jaddada buƙatar ƙarfafa haɗin kai tsakanin gwamnati, da jami’an tsaro, da al’umma baki ɗaya, domin tabbatar da an hana afkuwar irin wannan mummunan lamari a nan gaba.



