Tsohon shugaban karamar hukumar Kumbotso Kabiru Ado Fanshekara Ya Nuna Alhini kan Kisan Gillar da’akayi a Kumbotso

Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso kuma tsohon Mataimaki na Musamman ga tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, Kabiru Ado Fanshekara, ya bayyana matuƙar alhininsa kan kisan gillar da aka yi wa wasu bayin Allah a yankin.
A cikin wata sanarwa, Fanshekara ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda lamarin ya shafa, yana mai bayyana kisan a matsayin abin takaici da ba a saba gani ba a Karamar Hukumar Kumbotso.
Ya buƙaci Allah Maɗaukakin Sarki Ya jikan mamatan, Ya kuma bai wa iyalansu haƙurin jure wannan babban rashi.
Ya kuma yaba wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa nuna damuwa da kulawa kan abin da ya faru, tare da jinjinawa rundunar ƴansandan Najeriya bisa ƙwazon aiki da ya kai ga kama waɗanda ake zargi da hannu a kisan.
Fanshekara ya jaddada buƙatar haɗin kai tsakanin gwamnati da al’umma domin hana afkuwar irin wannan mummunan lamari a nan gaba.




