Labarai
An kama wadanda da ake zargi da hannu a kisan wata mata da ‘ya’yanta shida a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar da kama wasu mutane uku da ake zargi da kitsa kisan wata mata da ‘ya’yanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi da ke Kano a ranar 17 ga watan Janairun 2026.
An kama wadanda ake zargin, Umar Auwalu, Isyaku Yakubu, da Yakubu Abdulaziz, a wani samame da jami’an ‘yan sanda suka kai tsakanin daren ranar 17 ga watan Janairu zuwa ranar 18 ga watan Janairun 2026.
Majiyar tace tunu wanda ya jagoranci wannan mummunan aikin mai suna Umar Auwalu, wanda dan uwan marigayiyar ne, ya amsa laifinsa.
An samo wasu kayayyaki daga hannun wadanda ake zargin da suka hada da wayoyin hannu guda biyu na marigayiyar, adda, da kuma wasu makamai masu hadari.




