Labarai

Rundunar ‘yan sanda ta fara bincike akan Kashe Wata Mata Da ‘Ya’yanta Shida a Jihar Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kisan wata mata, Fatima Abubakar, mai shekaru 35, tare da ‘ya’yanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi da ke cikin birnin Kano.

Wani rahoto da rundunar ta fitar ya nuna cewa wasu miyagu da ba a san ko su waye ba sun kutsa gidan Haruna Bashir da misalin karfe 12:10 na ranar 17 ga Janairu, 2025, inda suka kashe iyalansa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa tuni an aike da jami’ai zuwa wurin da lamarin ya faru kuma an kwashe gawarwakin zuwa asibitin kwararru na Murtala Mohammed.

A halin yanzu, rundunar ta ce sashen binciken manyan laifuka (CID) ya fara gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata wannan danyen aikin tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

 

Haka kuma, rundunar ta mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan mamatan da al’ummar yankin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button