Labarai

Gwamnatin Kano Za Ta Ci Gaba da Horar da ’Yan Jaridan Yanar Gizo domin samun cigaba a jihar

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana aniyarta ta ci gaba da bai wa ’yan jaridan kafafen yada labarai na yanar gizo (online media) horo, domin inganta ƙwarewarsu da tabbatar da gudanar da aikin jarida bisa doka da ƙa’ida.

 

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’amuran Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan yayin buɗe taron bita na kwanaki biyu da gwamnatin jihar ta shirya wa Kano Online Media Chapel, wanda yake gudana a Jihar Jigawa.

 

A cewarsa, an shirya taron ne domin ƙara wa ’yan jaridan online ilimi da ƙwarewa, tare da tabbatar da cewa suna gudanar da aikinsu cikin nasara ba tare da karya doka ba.

 

 Ya yabawa ƙungiyar bisa rawar da take takawa wajen wayar da kan al’umma da tallafa wa manufofin ci gaban da gwamnatin Kano ta sanya a gaba.

 

Kwamishinan ya kuma ja hankalin ’yan jaridan da su guji wallafa labaran da ka iya haddasa tashin hankali ko barazana ga zaman lafiya a cikin al’umma.

 

A nasa jawabin, Shugaban Kano Online Media Chapel, Kwamared Abubakar Abdulkadir Dan Gambo, ya ce aikin jarida ta yanar gizo na fuskantar ƙalubale iri-iri, lamarin da ya sa horo ya zama wajibi domin kare mambobi daga fadawa cikin matsaloli.

 

Ya ƙara da cewa irin wannan horo na taimakawa wajen kauce wa yaɗa labaran ƙarya, tare da inganta sahihanci da ƙwarewa a aikin jarida. 

 

Ya kuma bayyana cewa duk da Kano ce ta fara kafa irin wannan ƙungiya a Arewa, sauran jihohi na fara yin koyi da ita.

 

An gabatar da muƙalu da dama a yayin taron, da nufin inganta aikin jarida da kuma hana duk wani aiki da ka iya haddasa tarzoma a tsakanin al’umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button