NDLEA ta kama mutane 538, ta kwace kilo 947 na kwayoyi a Jigawa

Hukumar Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi ta ƙasa (NDLEA) a Jihar Jigawa ta bayyana cewa ta kama mutane 538 tare da kwace kwayoyi masu nauyin kilo 947 a shekarar 2025, da darajarsu ta kai Naira biliyan 2.5.
Kwamandan hukumar, Hassan Kaboju, ya bayyana hakan yayin baje kolin kayan da aka kwace a Dutse.
Kaboju ya ce kwayoyin da aka kama sun hada da tabar wiwi, tramadol, diazepam, da wasu sinadarai kamar formalin da matasa ke amfani da su ba bisa ka’ida ba.
Ya kara da cewa wasu kwayoyin sun fi ƙarfin da likitoci ke amincewa da su, abin da ke jefa lafiya cikin haɗari.
Kwamandan ya bayyana cewa mutane 136 sun riga sun samu hukunci a kotu, yayin da ake ci gaba da shari’a kan wasu 115.
Haka kuma, NDLEA ta tallafa wa mutum 552 ta hanyar jinya da shawarwari, ciki har da maza 533 da mata 19.




