Labarai
Kotu ta yankewa Abubakar Alhaji Sabo hukuncin kisa ta hanyar rataya

Babbar Kotun Jihar Kano, ƙarƙashin Mai Shari’a Aisha Ya’u, ta yanke wa Abubakar Alhaji Sabo hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin kashe jaririn da ya haifa tare da budurwarsa.
Gwamnatin Jihar Kano ce ta gurfanar da shi kan zargin kisan kai da haddasa munanan raunuka.
Kotun ta gano cewa Abubakar Sabo ya ba wa jaririn fiya-fiya bayan budurwarsa ta ƙi amincewa da kashe shi, sannan ya jikkata mahaifiyar jaririn ta hanyar buga mata bulo a kai.
Bayan sauraron shaidu da hujjojin bangarorin biyu, kotu ta same shi da laifin kisan jariri tare da yanke masa hukuncin kisa, tare da karin hukuncin ɗaurin shekaru uku kan laifin haddasa rauni.




