Labarai

’Yan Sanda Sun Cafke Matasa Biyu Bisa Zargin Yunƙurin Kashe Mahaifinsu a Kaduna

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta cafke wasu matasa biyu da ake zargi da yunƙurin kashe mahaifinsu ta hanyar yi masa barazana da bindiga ƙirar gida a Karamar Hukumar Kauru ta jihar.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar ga manema labarai.

 

A cewar sanarwar, wani mutum mai suna Sunday Auta, mai shekaru 57, daga garin Galadimawa da ke Karamar Hukumar Kauru, ne ya kai ƙorafi ofishin ’yan sanda, inda ya zargi ’ya’yansa biyu — Benjamin Sunday wanda aka fi sani da Tigo, da kuma Monday Auta — da karya ƙofar ɗakinsa tare da yi masa barazanar harbi da bindiga ƙirar gida.

 

Rundunar ta bayyana cewa bayan cafke matasan, sun amsa laifin da ake tuhumarsu da shi, inda suka ce sun aikata hakan ne sakamakon wata takaddama da ta shiga tsakaninsu da mahaifinsu, don haka suka yi niyyar “koya masa darasi”.

’Yan sandan sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, kafin daga bisani a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu domin fuskantar hukunci bisa ga doka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button