Kotu Ta Bada belin Tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami da Iyalinsa akan Naira Miliyan 500

Kotun Tarayya da ke Abuja, ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Emeka Nwite, ta amince da bayar da beli ga tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami, tare da iyalinsa, a kan kuɗin naira miliyan 500.
Kotun tace belin zai kasance ne tare da mutum biyu da za su tsaya musu, inda alƙalin ya jaddada cewa masu tsaya wa belin dole ne su kasance masu filaye a yankunan Asokoro, Maitama ko Gwarinpa a Abuja.
Haka kuma, kotun ta umurce su da su miƙa dukkan takardun tafiyarsu (passport) ga kotu.
Wannan hukunci ya biyo bayan tuhume-tuhume da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta shigar a kwanakin baya, inda ta gabatar da tuhuma 16 a kan Malami da iyalinsa, da suka shafi zargin halasta kuɗaɗen haram da kuma mallakar kadarori da darajarsu ta haura naira biliyan 8.7.
Sakamakon waɗannan tuhume-tuhume ne dai aka tsare Malami da iyalinsa a gidan yarin Kuje da ke Abuja, kafin kotun ta amince da belinsu.
Ana sa ran shari’ar za ta ci gaba a wani lokaci da kotu za ta sanar, yayin da bangarorin ke shirin gabatar da hujjoji a gaban kotu.




