Labarai

‘Yan kasuwar man sun bukaci gwamnatin tarayya da ta aiwatar da matakan gaggawa na hana farashin man fetur da dizal su yi tsada ga ‘yan Najeriya.

Yayin da rikici tsakanin Iran da Isra’ila ke ci gaba da shafar kasuwannin mai a duniya, ‘Yan kasuwar man sun bukaci gwamnatin tarayya da ta aiwatar da matakan gaggawa na hana farashin man fetur da dizal su yi tsada ga ‘yan Najeriya

Duk da cewa farashin danyen man ya fadi kasa da dalar Amurka 70 a kowace ganga a ranar Talata, amma hauhawar farashinsu na baya-bayan nan, sakamakon tashe-tashen hankula a yankin Gabas ta Tsakiya, tuni ya fara yin tasiri a kasuwannin cikin gida.

Yayin da karin farashin da aka yi a baya-bayan nan kafin faduwar ranar Talata ya bayar da damar yin kiyasin kudaden shigar da gwamnati ke samu na dala 75 kan kowacce ganga, hakan kuma ya haifar da karin farashin kayayyakin man fetur da aka tace daga manyan kamfanonin da suka hada da matatar man Dangote.

Yayin da farashin danyen man fetur ya tashi daga kusan dala 66 zuwa kusan dala 80 kan kowacce ganga a baya-bayan nan, kafin zagayowar ranar Talata, masu sharhi sun yi gargadin cewa ‘yan Najeriya na iya fuskantar tashin farashin man na iya haura Naira 1,000 kan kowace lita, matukar ba a dauki matakai masu inganci ba.

Don haka ne ‘yan kasuwa ke kira ga gwamnatin shugaba Bola Tinubu da ta bullo da hanyoyin da za su tabbatar da cewar man yayi sauki ga masu karamin karfi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button