‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kasuwar Daji a Borgu, Jihar Neja

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari Kasuwan Daji da ke ƙauyen Demo, a Ƙaramar Hukumar Borgu ta Jihar Neja, da yammacin ranar Asabar, 3 ga Janairu, 2026.
Rahotanni sun nuna cewa maharan, waɗanda ake kyautata zaton sun fito ne daga dausayi da ke yankin Kainji Lake National Park, sun mamaye kasuwar da yamma, inda suka wawure kayayyaki da abinci na miliyoyin kuɗaɗe, kafin daga bisani su ƙone dukkanin shagunan da ke kasuwar.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce harin ya jefa ‘yan kasuwa da mazauna yankin cikin firgici.
SP Abiodun ya kuma bayyana cewa, ba a samu asarar rai ba, haka kuma ba a sace kowa ba yayin harin.
Rundunar ‘yan sanda ta ce ta fara bincike tare da ɗaukar matakan tsaro domin hana sake faruwar irin wannan hari a yankin.
Ya ƙara da cewa za a sanar da jama’a da zarar an samu ƙarin bayani game da lamarin.




