Labarai

EFCC Ta Yi Watsi da Zargin Bala Mohammed yayi mata

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashin Da’a ta Ƙasa (EFCC) ta ƙaryata zargin da Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi na cewa ana amfani da hukumar wajen tsananta masa da wasu daga cikin jami’ansa ta hannun abokan hamayya na siyasa.

 

EFCC ta bayyana zargin a matsayin marasa tushe, tana mai jaddada cewa hukuma ce mai zaman kanta wadda ke gudanar da aikinta ba tare da nuna bambanci ko biyayya ga wata jam’iyya ba.

Hukumar ta kuma ce babu wani jami’in siyasa da ke da ikon yin katsalandan a bincikenta.

Hukumar ta tunatar da cewa Bala Mohammed na fuskantar shari’ar safarar kuɗi tun kafin ya zama gwamna, amma kariyar kundin tsarin mulki ce ta dakatar da shari’ar. EFCC ta ƙara da cewa shari’o’in da ake yi wa wasu jami’an gwamnatin Bauchi sun dogara ne da sahihan bincike, ba ramuwar gayya ba.

EFCC ta yi kira ga ‘yan siyasa da su fifita gaskiya da riƙon amana, tare da barin hukumar ta ci gaba da aikinta na yaƙi da cin hanci a ƙasar nan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button