Labarai
Biyo bayan Umarnin Kwamishinan ‘yan sandan kano na hana Guje Guje da Motoci, Babura, da Kuma hawa Dawakai domin Kilisa

Kungiyar Mahaya Dokuna ta Jihar kano wato Kano Horse Riders Forum ta goyi bayan Umarnin Kwamishinan yan sanda akan wannan doka.
Shugaban Kungiyar Mahaya Dokuna ta Jihar kano Umar Abdulmumin ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da wakilin mu a wannan rana.
Yana Mai cewar Babu shakka Kungiyar su zasu hada kai da jami’an tsaro na yan sanda domin tabbatar da kudirin Kwamishina wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a fadin Jihar




