Siyasa
Atiku Ya yi Maraba da Komawar Peter Obi ADC

Tsohon ɗan takarar shugabancin kasarnan a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce yana maraba da komawar tsohon ɗan takarar jam’iyyar Labour, Peter Obi, cikin jam’iyyar haɗaka ta ADC.
Atiku ya bayyana hakan ne a shafukan sada zumunta, inda ya ce matakin Obi na da muhimmanci wajen ƙarfafa haɗakar da ke da burin ƙalubalantar jam’iyya mai mulki da kuma samar da mulki nagari a Najeriya.
Ya ƙara da cewa yana fatan komawar Obi za ta buɗe ƙofa ga sauran ‘yan siyasar da ke da kishin ƙasa domin haɗa kai wajen kawo ci gaba da zaman lafiya.



