Abdullahi Zubairu Abiya Ya Zama Mukaddashin Shugaban NNPP na Kano

Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano ta naɗa Hon. Abdullahi Zubairu Abiya a matsayin Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar na jiha, bayan tsige tsohon shugaban jam’iyyar, Hashimu Dungurawa.
An amince da naɗin Abiya ne bayan taron gaggawa da Kwamitin Zartarwa na Jiha (EXCO) ya gudanar a sakatariyar jam’iyyar da ke Kano, inda Barrista Yusuf Mukhtar, Mataimakin Mashawarcin Shari’a na jam’iyyar, ya bayyana cewa naɗin ya yi daidai da kundin tsarin mulkin NNPP.
Rahotanni sun nuna cewa matakin ya biyo bayan miƙa rahoton tsige da korar Dungurawa da Kwamitin Zartarwa na Karamar Hukumar Dawakin Tofa ya yi, wanda ya samo asali daga kudurin da Kwamitin Zartarwa na Unguwar Gargari ya amince da shi bisa zargin aikata ayyukan da suka sabawa jam’iyya.
Bayan nazarin rahoton, Kwamitin Zartarwa na Jiha ya amince da shi tare da tabbatar da Abiya a matsayin Mukaddashin Shugaba, matakin da jam’iyyar ta ce an ɗauka ne domin dawo da ɗa’a, ƙarfafa haɗin kai da kuma sake tsara jam’iyyar domin tunkarar kalubalen siyasa na gaba a Kano.
A nasa jawabin, Hon. Abdullahi Zubairu Abiya ya tabbatar da biyayyar jam’iyyar ga jagoran ta na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da kuma Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf.




