Dino Melaye Ya Yi Martani Kan Gurfanar da Tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami A gaban Kotu

Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya yi martani kan gurfanar da tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami (SAN), a gaban kotu bisa zargin handame kuɗaɗe da halasta kuɗin haram.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Melaye ya ce shari’ar da ake yi wa Malami ta tunatar da shi irin ƙalubalen da ya fuskanta a lokacin da Malami ke rike da muƙamin Ministan Shari’a, inda ya bayyana cewa a wancan lokaci ana gurfanar da shi bisa tuhumce-tuhumcen siyasa.
Duk da haka, Melaye ya ce yana yi wa Malami fatan alheri, yana mai jaddada cewa rayuwa tana da juyayi, kuma kowa na iya tsinci kansa a irin wannan hali a wani lokaci.
Rahotanni sun nuna cewa Hukumar EFCC ta gurfanar da Abubakar Malami tare da ɗansa Abdulaziz, matarsa da wani mutum a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja kan tuhume-tuhume guda 16 da suka shafi handame kuɗaɗe da mallakar dukiyoyi ta haramtacciyar hanya.
Wadanda ake tuhuma sun musanta laifukan da ake zargin su da su, yayin da kotu ta bayar da umarnin tsare su a gidan gyaran hali na Kuje, tare da dage sauraron buƙatar beli zuwa ranar 2 ga Janairu, 2026.



