Labarai
A’isha Buhari ta yi zargin ana bibiyarta ba tare da yardartaba

Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Hajiya A’isha Muhammadu Buhari, ta bayyana cewa wani babban malamin addinin Musulunci na bibiyarta tare da neman kusanci da ita ba tare da yardarta ba.
Ta bayyana hakan ne ta cikin wani saƙo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, inda ta nuna ɓacin ranta tare da gargaɗin cewa idan lamarin bai tsaya ba, za ta fito fili ta bayyana abin da ta sani a kansa.
A’isha Buhari ta bayyana mamakinta kan yadda mutum da ake kallonsa a matsayin jagora a addini zai aikata irin wannan ɗabi’a.




