Siyasa

Shugaban NNPP Ya Magantu Kan Jita-jitar Sauya Sheƙar Gwamna Abba Zuwa APC

*KANO, NAJERIYA** – Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Hon. Suleiman Hashim Dungurawa, ya bayyana cewa duk wani yunƙuri na Gwamna Abba Kabir Yusuf na komawa jam’iyyar APC, ra’ayinsa ne na kashin kai, ba matsayar jam’iyya ba.

 

Dungurawa ya bayyana hakanne a ranar Litinin yace Jagoran jam’iyyar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da shugabannin NNPP ba su amince da wannan sauya sheƙa ba.

 

 

Ya ƙara da cewa jam’iyyar ta yi iya ƙoƙarinta wajen nasiha ga gwamnan domin ya mutunta amanar jama’ar Kano, amma har yanzu abubuwa ba su canza ba.

 

A cikin sanarwar, shugaban jam’iyyar ya roƙi gwamnan da ya “mayar da wuƙarsa kube” ya tsaya a NNPP, yana mai cewa jama’a sun riga sun yi watsi da APC. Haka zalika, ya karyata zargin cewa shi ko wasu jiga-jigan jam’iyyar ne ke haifar da saɓani tsakanin Gwamna Abba da Kwankwaso, inda ya ƙalubalanci masu iƙirarin haka da su fito da hujja.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button