Mataimakin gwamnan jihar kano Aminu Abdulsalam, na iya zama mutum na farko da zai faɗa cikin guguwar siyasar da ke shirin afkawa jam’iyyar NNPP a Kano

Majiyoyi sun ce a matsayin wani ɓangare na shirin gwamnan na samun goyon bayan manyan jiga-jigan APC a Kano, ana shirin miƙa sunan tsohon ɗan takarar mataimakin gwamna na APC a zaɓen 2023, Murtala Sule-Garo, domin maye gurbin Abdulsalam. Haka kuma, ana shirin miƙa sunan tsohon ɗan takarar gwamna na APC a 2023, Nasiru Gawuna, a matsayin ɗan takarar Sanata na Kano ta tsakiya a 2027.
Tun bayan hukuncin Kotun Koli kan zaɓen gwamnan Kano, gwamnan ya yi ƙoƙari sosai wajen shawo kan Kwankwaso da ya koma APC.
A watan Nuwamban bara, DAILY NIGERIAN ta rawaito rikicin da ke ƙara tsananta a NNPP ta Kano, inda gwamnan ya kaurace wa taruka tare da ƙin ɗaga kiran wayar ubangidansa, Rabiu Kwankwaso.
A shekarar 2024, taken siyasa na “Abba Tsaya da Kafarka” — wato Abba, tsaya da ƙafarka, ko kuma a ma’ana mafi ƙarfi, Abba, rabu da Kwankwaso — ya yi fice a Kano, yayin da kiraye-kiraye daga cikin jam’iyyar da wajen ta ke ƙara ƙarfi na neman gwamnan ya zama mai cin gashin kansa.
Gwamnan, duk da ya sha alwashin biyayya ga Kwankwaso, ya musanta rahotonmu na Nuwamba 2024 tare da nesanta kansa daga ƙungiyar Abba Tsaya da Kafarka.




