Labarai
Rahoto: Gwamnan Kano na shirin komawa APC, Kwankwaso zai ci gaba da zama a NNPP

Rahotanni na nuni da cewa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kammala shirin sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC gabanin zaɓen 2027, bayan kammala tattaunawa da wasu daga cikin na kusa da shi a siyasance.
Sai dai, an ce jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ƙi amincewa da sauyin sheƙar, inda ya jaddada cewa zai ci gaba da zama a jam’iyyar NNPP.
Wani ɗan majalisar dokokin jihar ya bayyana cewa gwamnan ya sanar da wasu ’yan majalisa shirin nasa, yayin da ake sa ran magoya bayan Kwankwaso za su fitar da sanarwar nuna goyon baya gareshi da jam’iyyarsa.
Har zuwa lokacin kammala rahoton nan, ba a samu martani daga ɓangarorin gwamnan Kano ko Sanata Kwankwaso ba.




