Labarai

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da fara aiwatar da sabbin dokokin haraji daga 1 ga Janairu, 2026

Shugaban Kwamitin na Ƙasa Mista Taiwo Oyedele, ya tabbatar da cewa sabbin dokokin haraji za su fara aiki a ranar 1 ga watan Janairun 2026, kamar yadda aka tsara.

Oyedele ya bayyana hakan ne bayan ya yi wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bayani a Legas, inda ya ce an tsara sauye-sauyen dokokin ne domin rage wa ’yan Najeriya radadin tsadar rayuwa da nauyin da ke kansu, ba wai don tara kuɗaɗen shiga cikin gaggawa ba.

Ya ce gwamnati na da niyyar aiwatar da sauye-sauyen ne cikin tsari da fahimta, domin amfanin al’umma baki ɗaya.

Wannan matsaya ta Gwamnatin Tarayya na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan zargin yin gyare-gyare a cikin dokokin harajin da aka wallafa, bayan da Majalisar Wakilai ta zargi an yi mata shisshigi a kan tanade-tanaden dokokin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button