Siyasa

Tinubu Ya Taya Ganduje Murnar Cika Shekaru 76

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa kuma shugaban hukumar kula da filayen jiragen sama ta Tarayya (FAAN), Dr.

Abdullahi Umar Ganduje, murnar cika shekaru 76 da haihuwa.

 

A sakon taya murna da ya aike masa, Tinubu ya bayyana Ganduje a matsayin gogaggen ɗan siyasa kuma ƙwararren mai gudanarwa da ya shafe fiye da shekaru 50 yana hidimar al’umma da bunƙasa ƙasa.

Shugaban ƙasar ya tuna da tarihin Ganduje a harkokin mulki, inda ya ambaci mukaman da ya riƙe daga jami’in gwamnati a FCT, kwamishina a Kano, mataimakin gwamna na wa’adi biyu, zuwa gwamnan Kano na wa’adi biyu.

 

Tinubu ya kuma yaba da rawar da Ganduje ya taka a siyasar APC da kuma ayyukansa a halin yanzu a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa na FAAN, tare da yi masa addu’ar samun lafiya da tsawon rai domin ci gaba da hidimar Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button