Isra’ila da Iran sun amince da tsagaita wuta a yayin da kasashen ke cigaba da kai hari da makamai masu linzami

Rahotanni na cewa Iran da Isra’ila sun amince da tsagaita wuta bayan kwana 12 suna musayar hare-haren sama masu tsanani, ciki har da wani hari na “mintuna na ƙarshe” da Tehran ta kai.
Firaministan Israel Benjamin Netanyahu ya ce a cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar Talata cewa Isra’ila ta amince da tayin tsagaita wuta yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar a daren jiya. A baya, gidan talabijin na kasar Iran ya ruwaito cewa an fara tsagaita wutar.
Bayanin na ƙasar ta Isra’ila ya zo ba da jimawa ba bayan Trump ya ce a cikin wani sakon sada zumunta cewa an fara tsagaita wuta.
Yayin da Netanyahu ya yi barazanar cewa Isra’ila za ta mayar da martani da karfi ga duk wani take hakkin tsagaita wuta, yarjejeniyar ta haifar da fata na rage tashin hankali a rikicin da ya kara tsananta a ‘yan kwanakin nan, yayin da Amurka ta kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran kuma Tehran ta kai hari kan sansanin Amurka a Qatar.




