Ketare
Jami’an Iran na tattaunawa da Shugaba Putin na Rasha

Ministan harkokin wajen Iran ya kai ziyara Rasha tare da rakiyar wasu jami’an gwamnatin ƙasarsa, inda ya je domin ganawa ta musamman da Shugaban Ƙasar Vladimir Putin.
Abbas Araghchi ya yaba wa shugaban na Rasha, wanda ya ce tarihi ba zai manta da shi ba bisa jajircewar da ya nuna wajen fitowa fili ya yi Allah-wadai da harin Amurka a cibiyar nukiliyar Iran.
Ministan ya zargi Amurka da yi wa dokokin duniya da yarjejeniyar makamin nukiliya ta Non-Proliferation Treaty (NPT) karan tsaye ta hanyar ɗaukar matakin kai harin.



