Ketare

Fararen hula sun yi garkuwa da sojoji a Colombia

Sojojin ƙasar Colombia sun ce yanzu haka fararen hula sun yi garkuwa da sojoji 57 a yankin Micay da ke kudu maso yammacin kasar.

A wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafukan sada zumunta, ta ce an yi garkuwa da sojoji 31 a ranar Asabar yayin da sauran aka ɗauke su jiya Lahadi.

Sojojin sun ce fararen hular na ɗaukar wannan mataki ne sakamakon matsin lamba da suke fuskanta daga ƴan tawayen kungiyar FARC da ke yankin.

Yankin na ɗaya daga cikin yankunan da gwamnatin Colombia ke ci gaba da artabu da wasu tsirarun ƴan tawaye na ƙungiyar FARC da ke tayar da ƙayar baya tun bayan da akasarin ƙan kungiyar suka ajiye makamansu a shekara ta 2017.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button