Labarai
Netherlands ta mayar da mutum mutumin guda 119 da aka sace daga Nijeriya

Ƙasar Netherlands ta mayar da tsofaffin zane-zane na mutum mutumi guda 119 da aka sace daga tsohuwar masarautar Benin ta Najeriya fiye da shekaru 120 da suka wuce a lokacin mulkin mallaka.
Olugbile Holloway, darakta-janar na Hukumar Kula da Gidajen Tarihi da Abubuwan Tarihi ta Kasa ta Najeriya, ya ce a ranar Asabar cewa kayan tarihi suna “wakiltar asalin mutanen da aka ɗauke su daga gare mu.”
Holloway ya kara da cewa Jamus ta kuma amince da mayar da fiye da guda 1,000 na karin kayayyaki.
Kayayyakin tarihi, da aka sani da Benin Bronzes, sune na baya-bayan nan da aka mayar da su zuwa Afirka yayin da matsin lamba ke karuwa akan gwamnatocin Yammacin duniya don mayar da abubuwan da aka sace a lokacin mulkin mallaka.




