Mutane da dama sun mutu a wani harin ƙunar baƙin wake da aka kai jihar Borno

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ƴansandan jihar ASP Nahum Daso ya ce da misalin ƙarfe 10 na daren jiya Juma’a ne ƴar ƙunar baƙin waken ta kai harin da ya hallaka mutum 10, amma suna nan ana ci gaba da bincike kan lamarin.
Sai dai a wasu alƙaluma na daban da Zagazola Makama mai bin diddigin ayyukan ta’addanci a yankin ya fitar, ya ce mutum 24 ne suka mutu wasu da dama suka samu raunuka, a harin da wata ƴan ƙunar baƙin wake ta kai.
Makama ya ce an garzaya da waɗanda suka samu raunuka asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri UMTH, inda suke samun kulamar da ta kamata, sannan kuma ake ci gaba da tantance gawarwakin waɗanda suka mutu.
Tuni dai aka tura da jami’an tsaro da suka da sojoji da ƴansanda ciki harda masu warware bom da ƴan sakai, wurin da lamarin ya faru.
Harin ƙunar baƙin wake dai na daga cikin dabarun da maƙayan Boko Haram ke amfani da shi wajen kai hari, wanda kuma ya yi sanadiyar salwantar rayuka da dama.




