Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Nuna Aniyar Karɓar garin Ƙasar Kuyan Ta Inna Don Gina Jirgin Ƙasa a Kano

Duk da hukuncin kotu mai ƙarfi da ya hana Gwamnatin Tarayya, ta hannun Ma’aikatar Sufuri, karɓar ƙasar Kuyan Ta Inna da ke Kano, alamu na nuna cewa gwamnatin na ci gaba da shirin karɓar ƙasar domin aiwatar da aikin layin dogo.

Manoma da masu ƙasar har guda 75 ne suka gurfanar da Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya, kamfanin da ke kula da aikin jirgin ƙasa, da kuma hukumomin tsaro ciki har da Sojojin Najeriya a gaban kotu dangane da batun.

Sai dai a ranakun 19 da 20 ga watan Yuni, an rawaito cewa an ga ‘yan kwangilar aikin a wajen suna ƙoƙarin share fili domin ci gaba da aikin.

Wasu daga cikin masu ƙasar sun fuskanci wakilan aikin tare da nuna musu hukuncin kotu, amma wakilan sun ce ba su da masaniya game da hukuncin.

A ranar Asabar, an sake ganinsu a wurin suna ƙoƙarin karya umarnin kotu domin ci gaba da aikin share filin.

Rahoton Nigeria Tracker ya bayyana cewa yawancin ƙasar mallakar marasa galihu ne da marayu. Filayen da ke cikin tsarin gwamnati an kimanta su da fiye da naira miliyan biyar kowanne, amma hukumomin da ke gudanar da aikin na nuna rashin niyya wajen bin hukuncin kotu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button