Shugabar GIRS Ta Fito da Sabon Tsari Don Inganta Gudanar da Haraji

Shugabar Hukumar Karɓar Haraji ta Jihar Gombe (GIRS), Hajiya Aisha Adamu, ta jagoranci wani mahimmin taron tsara dabarun gudanarwa a hedkwatar hukumar domin ƙarfafa tsarin karɓar haraji
Wannan babban taron ya haɗa dukkan Shugabannin Sassa (HODs), inda suka duba ci gaban ayyuka, sake nazarin burin aiki, da tsara mafita ga ƙalubalen da ke hana ci gaba wajen tara kuɗaɗen shiga.
A jawabinta na buɗe taro, Hajiya Aisha ta yaba da ƙoƙarin shugabannin sassa da ma’aikatansu wajen gudanar da ayyukan tara haraji da samar da sabis cikin inganci.
Ta jaddada kudurin hukumar na gaskiya, amana da aiki tare don cimma burinta na samar da kuɗaɗen shiga.
“Taron nan wani dandali ne da muke amfani da shi wajen tantance nasarorin da sassa suka samu, gano matsalolin da ke hana aiki yadda ya kamata, da tsara mafita masu ɗorewa domin samun gagarumar nasara,” in ji ta.




