Ketare

Shugabannin mulkin soja na Nijar sun ce za su ƙwace kamfanin haƙar uranium na cikin gida mai suna Somaïr, wanda yawancin hannun jarinsa mallakin Faransa ne, a wani sabon mataki da ke ƙara tsananta rikicin diflomasiyya da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Somaïr yana ƙarƙashin ikon kamfanin Orano ne mallakin Faransa, wanda shugabannin Nijar ke zargi da aikata wasu “ayyuka marasa kishin ƙasa.

Tun bayan karɓar mulki a shekarar 2023, shugabannin sojin sun bayyana cewa suna son ƙarin ikon mallakar albarkatun ma’adinai na ƙasar, tare da nisantar Faransa wadda ita ce tsohuwar mai mulkin mallaka yayin da suke ƙara kusanci da Rasha.

Nijar ce ta bakwai a duniya wajen samar da uranium, kuma tana da ingantattun ma’adinai mafi daraja a nahiyar Afirka.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, Orano – wanda gwamnatin Faransa ke mallaka – ya shigar da ƙara kan matakin da gwamnatin Nijar ta ɗauka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button