Majalisar wakilai ta wanke jamhuriyar Togo daga zargin bada shedar karatun bogi a rikicin da ya barke a fannin ilimi shekarun da suka gabata.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kwamitin majalisar da ke kula da koke-koken jama’a ya mayar da hankalinsa ga jamhuriyar Benin, inda wata kungiyar da ake zargin ta kware kan aikin jabun satifiket din ke ci gaba da yin karfi.
Shugaban kwamitin majalisar mai kula da kararrakin jama’a, Bitrus Laori ne ya bayyana hakan yayin wani zaman binciken da aka ci gaba da yi a Abuja ranar Juma’a, biyo bayan karar da wata kungiyar masana sharia ta shigar a madadin manyan masu ruwa da tsaki a harkar ilimi.
Takardar koken ta yi tsokaci kan sanarwar da ma’aikatar ilimi ta tarayya ta yi a shekarar da ta gabata wanda ya shafi kasashen Togo da Jamhuriyar Benin na yin zamba a fannin ilimi.
A cewar Laori, binciken diflomasiyya daga ma’aikatar harkokin wajen kasar ya wanke Togo daga duk wani laifi, wanda ke tabbatar da sahihancin cibiyoyin ilimin kasar.

